Adobe Premiere Pro - Hausa
in CommunicationsCourse description
Koyon Adobe Premiere don Masu Fara – Umar Farook Usman
Wannan darasi yana koyar da yadda ake amfani da Adobe Premiere Pro cikin sauki ga masu farawa. Umar Farook Usman, ƙwararren mai shirya fina-finai da bidiyo, zai jagorance ku ta hanyoyin asali kamar yankan bidiyo, saka sautuka, gyaran launi, da ƙirƙirar bidiyo masu kayatarwa.
Idan kana so ka fara sana’a a fannin gyaran bidiyo ko kuma ka koyi dabarun ƙirƙirar bidiyo masu kyau, wannan darasi na Hausa zai taimaka maka sosai. Koyi dabarun gyara bidiyo cikin sauki da Hausa!